Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille sakataren jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro ya ce ƴan bindigar sun harbe illa har lahira a gidansa da daren ranar Litinin.
Da aka tuntube shi domin karin bayani mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce zai tuntubi baturen ƴan sanda kafin ya yi karin bayani.
Jihar Zamfara na cigaba da samun ƙarin hare-hare a ƴan kwanakin nan daga ƴan fashin daji dake ɗauke da makamai.
A cikin watan Maris ne gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa a yanzu jihar ta zama cibiyar ƴan fashin daji.