Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC sun bawa gwamnatin tarayya wa’adin ranar 31 ga watan Mayu kan ta janye ƙarin kuɗin wutar lantarki da suka yi.
Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana haka ne cikin wani jawabin bayan taro da suka fitar ranar Litinin a Abuja a ƙarshen wani taron gaggawa na haɗin gwiwa tsakanin shugabannin TUC da NLC.
A ranar 3 ga watan Afrilu ne hukumar ƙayyade wutar lantarki a Najeriya ta sanar da ƙarin wutar lantarki da ta ga masu amfani da wuta ta kasa su zuwa Rukunin A daga naira 66 kowane kilowatt ya zuwa ₦225.
Ƙarin ya jawo koke daga al’umma inda aka riƙa kiraye-kirayen a janye shi.
A jawabin bayan taron kungiyoyin sun ce matakin da gwamnati ta ɗauka ba tare da duba halin wahala da talakawa suke ciki bai dace ba kuma ɗora musu karin nauyi ne.
Ƙungiyoyin sun ce za su ɗauki matakin da ya dace matuƙar gwamnatin taki ta janye ƙarin.