Ƙarin wutar lantarki a Najeriya ƙuntata wa talaka ne – Ƙungiyar ƙwadago

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta soki matakin da gwamnati ta ɗauka na ƙara farashin wutar lantarki inda kilowat ɗin lantarki ya tashi daga naira biyu zuwa naira huɗu.

A baya-bayan nan ne dai hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki a ƙasar ta ɗauki matakin da ta ce an yi ne bisa la`akari da hauhawar farashi.

Ita dai ƙungiyar ta ce ƙarin farashin zai tsananta ƙuncin rayuwa da al`ummar ƙasar ke ciki, don haka ba za ta amince da shi ba.

Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta ƙasa Ayuba Wabba, a hirarsa da BBC ya yi Allah wadai da lamarin saboda “ƙarin da aka yi na baya-baya wajen Satumba, har yanzu ba a gama warware shi ba”.

Ya ce “ba a yi adalci ba bisa wannan cuta ta korona, yanzu ƙasashe tallafi ake ba talakawa, amma namu maimakon a taimaka, ana so a amshe abin da kake da shi.”

Wabba ya bayyana matsin da za a shiga sakamakon ƙarin kuɗin lantarkin – “masana’antu da kamfanoni masu zaman kansu wanda akasari su ne suke ɗan taimakawa a samu aikin yi, sun ce wannan abu zai shafe su”.

A cewarsa, wannan lamarin zai kuma shafi ma’aikatan gwamnati da masu karɓar pensho.

Ita dai ƙungiyar ƙwadagon ta ce ta fara yunƙuri kan yadda za ta ɓullowa lamarin kuma nan ba da jimawa ba ne za su gana kan batun.

Suma ƙungiyoyin farar hula sun soki matakin gwamnatin da tuni ya fara aiki ranar 1 ga watan Janairun 2021 inda suka ce salo ne na yaudara.

More from this stream

Recomended